Ministan harkokin wajen Katar Muhammed bin Abdurrahman Al Sani ya fıto karara ya bayyana cewa basu yarda da duk wanı shırın Isra'ila na mamaye yankin zirrin Gaza ba kuma zasu ci gaba da baiwa Falasdinawa gudunmowa da goyon baya.
Minista Al Sani, ya bayyana hakan a taron da aka gudanar ta bidiyo konferans mai taken ' Taimakawa Falasdinawa' ya kara da cewa,
Yankiz zirrin Gaza da Isra'ila suka kwashe kusan shekaru 30 suna shirin mallakewa ba zamu sanya ido mu yarda su mamaye wannan yankin ba.
Ministan Al Sani, ya jaddada cewa, Katar a cikşin shekaru 8 da suka gabata ta baiwa Falasdinawa gudunmowar dala biliyan 1.2, ında ya kara da cewa a 'yan kwanakın nan kuma ta baiwa Falasdin dala miliyan 150 domin taya ta yaki da corona.
Ya kara da cewa a cikin wannan yanayin na yaki da annobar corona Katar zata cigaba da baiwa Falasdin gudunmowa.