Kaso na 14 cikin darin wadanda suka kamu da Korona ma'aikatan lafiya ne

Kaso na 14 cikin darin wadanda suka kamu da Korona ma'aikatan lafiya ne

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta sanar da cewa kaso 14 cikin darin wadanda suka kamu da kwayar cutar Korona a doron kasa ma'aikatan lafiya ne.

Babban Daraktan WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sanar da cewa kaso 14 cikin darin wadanda suka kamu da kwayar cutar Covid-19 ma'aikatan lafiya ne.

Ghebreyesus, ya gana da manema labarai bayan taron da aka gudanar da yanar gizo a Geneva dak kasar  Switzerland, inda yake cewa,

"Wacanan annobar ta tunatar da mu duk irin jaruntakar aikin da kwararrun kiwon lafiya ke yi a kowace rana." 

 


News Source:   ()