An gano cewar kaso 80 cikin dari na masu dauke da cutar Corona (Covid-19) na da karancin sinadarin Vitamin-D.
Sakamakon binciken da aka gudanar a Spaniya kuma aka wallafa shi a mujallar "Journal of Clinical Endocrinology & Metabolism" an yi nazari kan alakar cutar Corona da karancin sinadarin Vitamin-D.
A karkashin binciken an gano kaso 80 cikin 100 na masu dauke da Corona su 216 na da karancin sinadarin Vitamin-D, kuma matsalar ta fi yawa ga mata.
Dr. Jos Hernandez na jami'ar Cantabria da ya ke daya daga cikin wadanda suka gudanar da binciken ya ce "Dole ne a bayar da shawara ga masu dauke da cutar Corona da aka gano suna da karancin Vitamin-D. Wannan na kara karin kashi da gabobi sannan yana taimaakwa wajen yakar cututtukan mura da dangoginsu.
Masanan kimiyyar sun bayyana cewar akwai alaka mai karfi tsakanin rasa rayukan da Corona ke janyowa da kuma karancin sinadarin Vitamin-D.