Kasar Bangladesh ta sanar da cewa kusan kashi 55 cikin darin wadanda suka kamu da kwayar cutar Covid-19 a kasar sun warke haka kuma yawan wadanda cutar ta yi ajali sun kai kaso 1.30 cikin dari.
Sanarwar ta kara da cewa a cikin ‘yan awanni da suka gabata mutum 1,768 sun warke lamarin da ya kara yawan wadanda suka warke daga cutar a jumlace zuwa dubu 120, 976 wato kaso 55.33 cikin darin wadanda suka kamu da ita kamar yadda jami’ar ma’aikatar lafiya Nasima Sultana ta shaidawa manema labarai.
Haka kuma an samu karin wadanda cutar ta yi ajali har su 35 da suka hada da maza 28 da mata bakwai inda yawan ya kai dubu 2,836.