Kaso 30 cikin darin iyalai basa iya ciyar da yaransu a Labanon

Kaso 30 cikin darin iyalai basa iya ciyar da yaransu a Labanon

Fiye da kashi 30 cikin darin iyalai a Labanon a wannan watan Maris suna da aƙalla yaro ɗaya wanda ke kwana da yunwa, a cewar wani sabon rahoton na hukumar UNICEF.

Rahoton Lebanon: Makomar yara, wanda aka fitar a wannan makon, ya yi nazarin tasirin rikicin tattalin arzikin Labanon ga yara.

Rahoton ya kuma jaddada cewa kashi 77 cikin darin  iyalai a Labanon din sun ce ba su da wadatar da za su sayi abincin da za su ciyar da ‘ya’yansu a wata, wadanan alkaluman suna karuwa har izuwa kaso 99 cikin dari ga yaran Siriyawa a kasar ta Labanon.

Da yake tabo batun rashin ingantacciyar kula da  jama'a a Labanon, ya bayyana cewa "kashi 60 cikin dari dole ne su sayi abinci a kan bashi ko kuma su ci bashi."


News Source:   ()