Taron ya kuma bayyana hadarin dake tattare da karuwar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya ce ci gaba da kai hare hare Gaza na sama da shekara guda ya sanya fadadar yakin zuwa Lebanon da kuma shafar kasashen Iraqi da Syria da kuma Lebanon, ya yin da duniya ta gaza daukar matakin kawo karshen yakin.
Shugabannin kasashen da suka halarci taron sun yanke hukuncin aiki tare domin goyan bayan ganin kasar Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba a Majalisar dinkin duniya, tare da bukatar kasashen duniya da su daina sayarwa Isra'ila da makamai.
Shugaban kasashen da suka halarci taron AFP - -Sanarwar bayan taron da aka gabatar ya yi Allah wadai da murya mai karfi a kan laifuffukan yakin da Isra'ila ta aikata a tzirin Gaza, wanda ta bayyana shi a matsayin kisan kare dangin da ya kunshi azabtarwa da kisan gilla da tilastawa jama'a bacewa tare da kawar da wani jinsi daga doran kasa.
Shugabannin sun kuma bukaci kwamitin sulhu da ya kafa wani kwamitin bincike na musamman a matakin duniya domin binciko irin laifuffukan da Isra'ila ta aikata tare da daukar mataki mai karfi wajen tabbatar da cewar ba'a boye wata shaida ba, sannan a tabbatar da hukunta duk wadanda aka samu da laifi.
Taron ya kuma bayyana bacin ransa da yadda Isra’ila ke bijirewa kudirin Majalisar dinkin duniya mai lamba 1701 da duk tanade tanaden dake cikin sa da ya shafi dakarun samar da zaman lafiyar dake kasar Lebanon wadanda dakarunta ke ci gaba da kai wa hari tare da hallaka fararen hular dake kasar.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a taron kasashen Musulmi da Larabawa a Riyadh © Saudi GazetteShugabannin sun ce ba zasu lamunta da yadda Isra’ilar ke yiwa Falasdinawa kudin goro ta na kai musu hari da kuma amfani da yunwa wajen azabtar da su ba, yayin da suka bukaci daukar matakn gaggawa wajen janye dakarun Isra’ilar dake daukacin yankin Gaza da kuma bude duk hanyoyin da ake amfani da su wajen shiga yankin.
Taron ya kuma bukaci kasashen duniya da su daina sayarwa Isra’ilar ko kuma kai mata makamai tare da bukatar kasashen duniya da su daina fuska biyu wajen mutunta kudirorin Majalisar dinkin duniya tare da dokokin duniya.
Shugabannin wadanda suka yabawa Algeria wajen gabatar da kudirori a kwamitin sulhu na amincewa da kasar Falasdinu sun ce zasu ci gaba da daukar duk matakan diflomasiyar da suka dace wajen ganin sun cimma wannan muradu na ganin kasar Falasdinu ta tabbata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI