Kasashen G7 za su tattauna akan Afghanistan

Kasashen G7 za su tattauna akan Afghanistan

Shugaban kasar Amurka Joe Biden zai tattauna kan Afghanistan a wa ta ganawa ta yanar gizo tare da shugabannin kasashen G7 (7 mafi karfin tattalin arziki) a ranar Talata.

A cikin rubutacciyar sanarwa, Kakakin Fadar White House Jen Psaki ta bayyana cewa shugabannin kasashen G7 (Jamus, Amurka, Birtaniya, Faransa, Italiya, Japan da Kanada da Tarayyar Turai) za su tattauna kan manufofin Afghanistan da daidaitawa kan kwashe al'umma daga babban birnin, Kabul.

Psaki ta bayyana cewa agajin jin kai ga Afganistan da tallafawa 'yan gudun hijirar Afghanistan suma za su kasance cikin ajandar taron.


News Source:   ()