Kasashen duniya sun fara martani kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Kasashen duniya sun fara martani kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump shi ya fara sanar da kulla yarjejeniyar, inda ya wallafa cewar an kulla yarjejeniyar domin sakin Yahudawan da aka yi garkuwa da su a Gabas ta Takiya, kuma nan bada dadewa ba za'a sake su.

Trump ya kara da cewar bayan yarjejeniyar, tawagar shugabanin tsaronsa tare da Jakada na musamman a Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff zasu ci gaba da aiki da Israila da kuma kawayensu wajen tabbatar da cewar Gaza bata sake zama sansanin 'yan ta'adda ba.

Shi kuwa ministan harkokin wajen Turkiya, Hakan Fidan cewa ya yi yarjejeniyar na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar yankin, yayin da ya jaddada matsayin kasarsa na ci gaba da fafutukar kafa kasar Falasdinu.

Firaministan Belgium Alexander de Croo yace yarjejeniyar za ta basu damar numfasawa saboda irin halin kuncin da wadanda akayi garkuwa da su da kuma iyalansu ke ciki, tare da mutanen Gaza.

Kungiyar kasashen Turai ta hannun kwamishinanta Dubravka Suica ta jinjinawa yarjejeniyar tsagaita wutar, yayin da ta ce EU za ta ci gaba da goyan bayan shirin tabbatar da zaman lafiya da farfado da yankin.

Isra'ila wadda ta ce an kashe mata sojoji 408 a yakin, ta bayyana cewar ba zata fice daga Gaza ba har sai Hamas ta saki daukacin Yahudawan da ta yi garkuwa da su.

Sakataren harkokin wajen Amurka mai barin gado Antony Blinken ya ce ya zama wajibi ga Isra'ila da ta amince da shirin hadewar Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan a karkashin ikon hukumar Falasdinawa tare da bada damar kafa kasar Falasdinu.

Firaministan Falasdinu Mohammed Mustafa ya ce yarjejeniyar ta tabbatar da tirsasawar da kasashen duniya suka yiwa kasar Israila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)