Malesiya ta fitar da sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon gobarar daji a yankuna daban -daban a kasar Turkiyya.
Ministan harkokin wajen kasar Hishamuddin Hussein, wanda ya yada a shafin sa na sada zumunta yace,
"Malesiya tana mika ta'aziyarta akan asarar rayuka sakamakon gobarar daji a yankin Antalya dake Turkiyya, ga takwarana na Turkiyya Mevlut Cavusoglu."
Hishamuddin Husaini ya kara da cewa,
"Addu'o'in mu suna tare da gwamnatin Turkiyya da mutanen ta a wannan mawuyacin lokaci."
Haka kuma kungiyar mai zaman kanta ta Malaysia mai ba da shawara kan kungiyar Musulunci ta Malaysia (MAPIM) ta bayyana hadin kai da jajantawa Turkiyya game da bala'in gobara.
Shugaban MAPIM Mohd Azmi Abdul Hamid ya bayyana cewa Malesiya na jin radadin da jama'ar Turkiyya ke ji.
Jordan ma ta fitar da rubutacciyar sanarwa cewa tana tare da Turkiyya, wacce ke yaki da gobarar daji.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Jordan Dayfullah al-Fayiz ya jajantawa 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a gobarar da ta afku a Turkiyya.
Fayiz ya ce Jordan na tare da 'yan uwan Turkiyya a wannan mawuyacin lokaci.
A gefe guda kuma, rukunin farko na kungiyoyin da ke da alaka da Ma’aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta Azabaijan sun zo Mugla don tallafawa yaki da gobarar daji.
Wasu gungun mutane 100, da suka isa filin jirgin saman Dalaman daga filin tashi da saukar jiragen saman Baku Heydar Aliyev, za su bayar da gudunmowa akan kokarin kashe gobarar.
Tarayyar Bosniya da Herzegovina (FBIH), daya daga cikin kungiyoyi biyu na Bosnia da Herzegovina, ta kuma sanar da cewa za ta aika da taimako don tallafawa shawo kan gobarar daji a yankuna daban -daban na Turkiyya.