Kasar Ostreliya ta janye dakarunta na karshe daga Afghanistan

Kasar Ostreliya ta janye dakarunta na karshe daga Afghanistan

Kasar Ostireliya ta cire jami'ai masu tallafawa sojoji 80 daga Afghanistan.

Ministan Tsaro kasar, Peter Dutton ya ce shiga tsakani ta kasarsa cikin yakin shekaru 20 da Afghanistan ya zo karshe.

Dutton ya kuma kara da cewa an cire jami'a masu bada tallafi 80 daga Afghanistan, kuma janye sojoji ya gudana a makonnin da suka gabata.

Da yake magana da tashar labarai ta Sky News, Dutton ya ce

"Wannan ba yana nufin cewa ba za mu kasance wani ɓangare na kamfen ɗin da aka yi tare da Amurka ba yayin da muke tunanin hakan yana cikin fa'idarmu ta ƙasa ko ta abokanmu." 


News Source:   ()