Kasa ta taushe masu hakar ma'adanai a jihar Benue dake Najeriya

Kasa ta taushe masu hakar ma'adanai a jihar Benue dake Najeriya

An sanar da cewa a rushewar ramin hakar zinarin da wasu ke yi ba bisa ka'ida ba a jihar Benue dake Najeriya an fara bayyana cewa mutum 7 sun rasa rayukansu. 

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Benue Catherine Anene, ta sanra da cewa a yankin Makurdi an samu rushewar ramin masu hakar ma'adanai.

Anene, ta kara da cewa a yayinda ake gudanar da aikin ceto an fara gano gawarwakin mutum 7 a yayinda ta kara da cewa ana ci gaba da aikin ceton.

Ana ikirarin cewa a Najeriya akwai masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida kuasan dubu 10 a fadin kasar.

 


News Source:   www.trt.net.tr