An sanar da cewa a rushewar ramin hakar zinarin da wasu ke yi ba bisa ka'ida ba a jihar Benue dake Najeriya an fara bayyana cewa mutum 7 sun rasa rayukansu.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Benue Catherine Anene, ta sanra da cewa a yankin Makurdi an samu rushewar ramin masu hakar ma'adanai.
Anene, ta kara da cewa a yayinda ake gudanar da aikin ceto an fara gano gawarwakin mutum 7 a yayinda ta kara da cewa ana ci gaba da aikin ceton.
Ana ikirarin cewa a Najeriya akwai masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida kuasan dubu 10 a fadin kasar.