Kasa ta taushe masu hakar ma'adanai 10 a kasar Nicaragua

Kasa ta taushe masu hakar ma'adanai 10 a kasar Nicaragua

An sanar da cewa akalla mutane 10 sun makale sakamakon rushewar gurin mahakar zinare a kudancin Nicaragua.

lamarin ya faru ne a inda ake ayyukan hakar zinare ba bisa ka'iada a iyakan kasar Costa Rica.

Shugabanin sun sanar da cewa akallan mutum goma kasa ta taushe sanadiyar zaftarewar inda ake hakar ma'adanan.

Mataimakin shugaban kasar Nicaragua Rosario Murillo ya sanar da cewa an aika ma'aikatan ceto yankin inda suka fara aiki nan take.

Murillo ya kara da cewa an yi nasarar kubutar da mutum daya wanda kuma yayi nasarar samaun wani zinare mai girma.

A dayan barayin kuma shugaban kasar Daniel Ortega ya bayyana cewa "muna fatan ba zamu samu wata masifar ba"
 

 


News Source:   ()