Karzai: Amurka ta gaza a Afghanistan

Karzai: Amurka ta gaza a Afghanistan

Tsohon shugaban kasar Afghanistan ya ce Amurka ta zo kasarsa ne don yaki da tsattsauran ra'ayi da kuma samar da kwanciyar hankali ga kasar amma bayan shekaru 20 da zata fice daga kasar ta gaza a dukkanin bangarorin biyu.

A wata hira da ya yi da kamfanin dillacin labarai na Associated Press 'yan makonni kafin sojojin karshe na Amurka da na NATO su bar Afghanistan, 'Hamid Karzai ya ce tsattsauran ra'ayi yana a "mafi girman matsayi" kuma sojojin da ke barin kasar suna barin wata masifa.

"Kungiyoyi sun zo nan shekaru 20 da suka gabata tare da wannan kyakkyawar manufa ta yaƙi da tsattsauran ra'ayi da kawo kwanciyar hankali ... amma tsattsauran ra'ayi shi ne a mafi girman matsayi a yau. Don haka sun gaza,"

 


News Source:   ()