
An cimma matsayar ce yayin ganawar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a Saudiya, zaman da Ukraine da kuma EU ba su samu goron gayyatar halartarsa ba.
Ganawar dai ita ce ta farko da aka yi tsakanin jami’an Amurka da Rasha, tun bayan ƙaddamar da mamayar Ukraine da shugaba Putin yayi a farkon shekarar 2022.
Buƙatar sake fasalin yarjeniyoyin tsaron Turai na daga cikin sharuɗɗan da Rasha ta ce dole a amince da su kafin a ci gaba da tattaunawar da aka fara domin kawo ƙarshen yaƙinta da Rasha.
Sai dai saɓanin yadda aka zata babu wani ƙarin bayani a kan yiwuwar ganawar kai tsaye tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.
A ranar Litinin Faransa ta karɓi baƙuncin taron shugabannin wasu manyan ƙasashen Turai a birnin Paris, duk dai kan makomar yaƙin na Rasha da Ukraine amma su ka gaza cimma matsaya guda kan matakin da Amurka ta ɗauka, na fara tattaunawa da Rasha ba tare da tuntuɓar su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI