An gabatar da korafe-korafe kusan dubu 93 na cin zarafin mata da Kungiyar Rainon Matasa ta Amurka (BSA), kungiyar horar da matasa mafi girma kuma mafi tsufa a Amurka ta yi.
Andrew Van Arsdale, daya daga cikin lauyoyin wadanda abin ya shafa wanda ya yi magana da CNN ya bayyana cewar za a iya gabatar da korafe-korafe har zuwa karfe 17:00 agogon yankin a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba kuma ya kara da cewa cin zarafin mata ya zama "dokar da ba a magana akai" a cikin BSA.
Arsdale ya ce ya tattaunawa na tsawon watanni 19 da dubun-dubatar wadanda aka ci zarafinsu kuma abubuwan da suka faru na musgunawa sun koma baya har zuwa shekarun 1960 a duk fadin kasar kuma ya zuwa yanzu an gabatar da kararraki 93,700 daga cikin wadanda suka koka.
Rubutacciyar sanarwar da BSA ta fitar game da zargin ta bayyana cewar ”Muna bakin cikin cewa ba za mu iya sassauta radadin wadanda suka bayyana korafinsu a lokutan baya ba."
BSA ta bayyana cewar tana fuskantar fatarar kudi ne a watan Fabrairu saboda nauyin diyyar da za ta biya, bayan kararraki da korafe-korafen cin zarafin da aka gabatar kan kungiyar a duk fadin kasar.
An kiyasta cewa ƙungiyar, wacce ke da tarihin shekaru 110, har yanzu tana da mambobi kusan miliyan 2 da ke da rajista kuma suna da kadarori tsakanin dala biliyan 1 zuwa 10.
An san BSA a ko'ina cikin ƙasar don sansanonin ilimi da aiyukan tarbiyyantar da matasa.