Kasar Siriya da yaki ya jefa cikin halin ha'ula'i na gab da fadawa cikin yunwa kasancewar miliyoyin al'umma ba su da abinci sakamakon tsananin karancin abinci a kasar kuma suna matukar bukatar agaji daga kasashen duniya.
Hussein Mahmoud, wani manomi da aka raba da muhallinsa daga lardin Hama na Siriya wanda yanzu yake zaune a wani sansani a arewacin Idlib, ya raba kayan yau da kullun a cikin kwandon abinci da yake karba duk wata tsakanin matarsa da ’ya’yansa 13.
Ganin cewa burodi, shinkafa, kayan lambu da sauran kayan masarufi da yake samu tsakiyar wata ya yi karanci, Mahmoud yana tsoron wannan ɗan tallafin da ya samar da hanyar tsira ga danginsa na iya ƙarewa. Inda yake bayyana cewa,
"Idan wannan taimakon abinci ya tsaya, ina za mu? Me za mu yi?" yace. "Yunwa na kan hanya."
Sabili da haka ya kamata kasa da kasa su ci gaba da kai gudunmowar abinci ga mabukata a kasar ta Siriya.