Wasu kanfunan sarrafa sutura a kasar Japan sun bayyana cewar zasu fara sarrafa tufafin da zai iya kashe kwayoyin cutar da ke sanya bil adama rashin lafiya.
Kanfunan na kasar Japan sun bayyana cewa ire-iren wadannan kayayyakin da zasu iya hallaka kwayoyin cutar baya ga kauda warin jiki ne zasu fara sarrafawa nan bada jimawa ba.
Suturan da kanfanin Murata Manufacturing zai yi ha hadain gwiwar kanfanin Teijin Frontier da dubbed PIECLEX zasu iya amfani da karfin lantarki ne da zai samu a yayinda mutum ya sanyasu a jikinsa kuma ya yi tafiya.
Kanfunan sun bayyana cewa lantarkin da suturan zasu yi amfani dashi bai da karfin da mai sanye da suturan zai jishi, amma kuma yana da karfin hallaka dukkanin virus, bakteriya da sauran kwayoyin cutar da ke iya yaduwa su sanya mutum rashin lafiya.
Mai magana da yawun kanfanin Murata ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Faransa ta AFP da cewa an gwada wannan sabon tsarin kuma nasararsa ta kai kaso 99 cikin dari akan virus da sauran kwayoyin halitta.
Kanfunan sun bayyyana cewa kayayyakin da zasu kansance hakan sun kunshi takunkuman rufe fuska, pampas, suturan masu motsa jiki, kayan ‘yan wasa da sauranasu.
A halin yanzu dai suna cigaba da aiki ba dare ba rana domin gano ko sabuwar tsarin zata iya kashe sabuwar kwayar cutar corona.