Kanfanin sarrafa magunguna a Amurka wato Pfizer ya nemi Indiya ta zama wacce zata siyar da rarraba alurar riga-kafin Covid-19 sanfarin "BNT162b2" da ya yi da kanfanin BioNTech na kasar Jamus.
A kasar Indiya da ake a mataki na biyar wajen gwajin wani allurar riga kafin na Korona wannan ne karon farko da wani kanfani ya nemi ta zama mai rarraba allurar riga kafin Korona.
A kasar ta Indiya allurar riga-kafin Korona da kanfanin kasar mai suna Bharat Biotech ya samar an fara gwajinsa a mataki na uku a fadin kasar ranar 27 ga watan Nuwamba.