Kanfanin jirgin saman kasar Singapore ya bayyana sallaman mutun 4,300 daga aiki sanadiyar matsalolin samnu kudaden shiga da kwayar cutar Covid-19 ta haifar.
Shugaban kanfanin Goh Choon Phong, ya bayyana cewa an dauki matakin ne sabili da cewa za’a dauki tsawon lokaci ba’a farfado ba kuma babu tabbacin akan samun mafita.
Ya kara da cewa mun kaim akura inda ya zama wajibi mu dauki wannan mawuyacin matakin. Wannan matakin na rabuwa da ma’aikatanmu ya kasance mafi wuyar hukunci da aka yanke a shekaruna na 30 ina aiki da kanfanin.