Hukumomin kasar Rasha sun sanar da cewa kanfanin jiragen saman kasar zai fara sintiri zuwa Turkiyya a ranar 1 ga watan Agusta.
Bayan dakatar da sufurin jiragen sama da aka yi sakamakon kwayar cutar corona za’a fara kai kawon jiragen saman daga manyan biranen Rasha uku da suka hada da babban birnin Moscow, Saint Petersburg, da Rostov-on-Don kamar yadda mataimakin firaiminista Tatyana Golikova ya shaidawa manema labarai a Moscow.
Jiragen Rasha zasu fara zuwa Ankara da Istanbul ne a ranar 1 ga watan Agusta daga bisani kuma su fara zuwa Antalya, Bodrum da Dalaman a ranar 10 ga watan Agusta.
Haka kuma zasu fara sintiri zuwa kasashen Gabashin Afirka, Birtaniya da Tanzaniya.