Kanfanin jirgin saman Pegasus ya sanar da cewa daga watan Agusta zai fara sintiri zuwa kasashe 17 da suka hada da kasar Rasha.
Kamar yadda hukumar Pegasus ta sanar kanfanin da ya fara sintiri zuwa kasashen waje a ranar 11 ga watan Yuli zai habaka kashashen da zai rinka zuwa daga watan agusta.
A bisa haka, a ranar 1 ga watan Agusta kanfanin zai fara kai da dauko fasinja daga Tbilisi a Georgia, Tehran a Iran, Baghdad da Erbil a Iraki, Doha a Katar, Bishkek a Kyrgyzstan, Hurghada da Sharm El Sheik a Masar, Moscow a Rasha, Krasnodar, Grozny da Mineralny Vody da Kuwait.
Kanfanin Pegasus din kuma daga ranar 2 ga watan Agusta zai fara sintiri zuwa zuwa Geneva a Switzerland, Hannover a Jamus da kuma zuwa Casablanca a Morocco a ranar 10 ga Agusta.
Haka kuma daga ranar 15 ga watan Agusta kanfanin zai fara sintiri zuwa " a Czechia-Prague, a Faransa-Marseille, a Italiya-Rome, a Spain-Barcelona da Madrid, a Hungary-Budapest, a Romania-Bucharest, a Saudiyya-Jeddah da Riyadh".