An sanar da cewa kanfanin jirgin saman IAG na kanfanin jirgin saman Birtaniya ya sanar da yin hasarar dala biliyan 4.5 sabili da matsalolin da kwayar cutar Covid-19 ta haifar.
Kungiyar kanfanin jirgin da ya bayyana samun riba na Euro miliyan 806 a bara ya bayyana wasu shirye-shiryen da zai kara masa kudaden shiga har Euro miliyan 2.75 domin kaucewa matsalolin da Covid-19 ta haifar.
Daga watan Febrairu 2020 dai kawo yanzu matsalkar Covid-19 ta shafi harkokin sufurin jiragen sama kwarai da gaske lamarin da ya haifar musu da hasarori masu yawa.