Kanfanin Apple zai fara kera motoci marasa matuka

Kanfanin Apple zai fara kera motoci marasa matuka

Kanfanin Apple na kusa da kammala yarjejeniya da kanfanin motocin Koriya ta Kudu wato Hyundai akan fara kera motoci marasa matuka.

Kafar yada labaran kasar Amurka ta CNBC ce ta rawaito cewa kanfanin na Apple na tattaunawa da kanfunan Hyundai na Kia domin fara kera motocin da za ta fara yi a yankin kudancin Gerogia.

Rahoton ya kara da cewa kanfanin na Apple ya jima yana nazarin fara kera motoci mallakar kansa da zasu rinka tafiya ba tare da matuka ba.

Kanfanin dillancin labaran Koriya ya rawaito cewa kanfanin Apple na bukatar sanya hannun jari na biliyoyin dala a cikin kanfanin Kia wanda za a bayyana a ranar 17 ga watan Febrairu kuma ta na shirin rinka kera motoci har dubu 100 a shekara daga shekarar 2024.

 

 

 

 


News Source:   ()