Elon Musk, mai kamfanin American Tesla, mai kera motocin lantarki, ya sanar da cewa a yanzu kamfanin zai fara kera mutum-mutumi.
Kamfanin ya fara aiki a kan kera mutum-mutumi da zai yi ayyuka a fannoni da dama.
Za'a kera robot din mutum-mutumin ne da fasahar da ake amfani da ita a kera motocin lantarki.
Robot din, wanda zai kasance da yatsun hannu guda biyar, an kera shi da tsayin santimita 177 da nauyin kilo 57.
Elon Musk ya nanata cewa robot din an tsara shi yadda zai fi dan adam rashin sauri.
A wannan shekarar ne aka fara samfara mutum-mutumin.