Kane wanda shine kyaftin din kasar Ingila ya jefa wadannan kwallayen ne a mintina 19 da 57 da 73 da kuma 78 a ci 9-2 da Munich ta yiwa Zagreb.
Daga cikin kwallaye 4 da Kane ya jefa, guda 3 sun samu ne ta hanyar fenariti, yayin da guda kuma ta samu a cikin wasa.
Wannan ya kawo adadin kwallayen da Kane ya ciwa Bayern Munich zuwa 53 tun bayan sauya shekar da ya yi a shekarar da ta gabata.
A wannan sabuwar kakar kawai Kane ya jefa kwallaye 9 a wasanni guda 6 da ya buga.
Tuni masu bibiyar harkokin kwallon kafa suka fara sharhi dangane da tagomashin da Kane ke da shi da kuma fatar ganin ya samu nasarar yin zarra a kakar bana.
Mai horar da 'yan wasan Munich Vincent Kompany ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan nasara ta Kean da kuma wadda kungiyar ta samu.
Kompany ya ce mutane sun fara ganin kokarin da yake yi domin sauya alkiblar kungiyar domin dawo da kimarta da kuma bunkasa rayuwar 'yan wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI