An bayyana cewa a fadin duniya, yawan ma’aikata yara ya kai miliyan 160.
Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO) da Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) sun bayyana cewa adadin yaran da ke aiki a matsayin ma'aikata ya karu da miliyan 8.4 a cikin shekaru hudu da suka gabata, lamarin kuma ya kai miliyan 160 a duniya.
Bautar da Yara: Dangane da hasashen na duniya ta 2020, yanayin da kuma rahoton halin da ake ciki a nan gaba, ana fargabar cewa yawan yara masu aiki zai tashi zuwa miliyan 169 a karshen shekarar 2022 idan ba a dauki matakan da suka dace ba.
Daga cikin yara miliyan 160 masu aiki, akwai yara miliyan 79 'yan tsakanin shekaru 5 zuwa 17 da ke aiki a cikin ayyuka masu hadari. Kaso 28 cikin dari na yara ‘yan shekara 5-11 da kaso 35 cikin dari na yara 'yan tsakanin shekara 12-14 ba sa zuwa makaranta.
Kaso 72 cikin darin dukkan yara masu aiki suna aiki tare da iyalansu. Akasin tunanin cewa yin aiki tare da iyali na iya zama lafiya, yara suna shiga cikin ayyuka masu haɗari koda kuwa sun yi aiki tare da iyalin su ne.
Duk da yake yawan bautar da yara ya ragu daga kashi 13.3 zuwa kashi 5.6 cikin dari a Asiya da yankin Pacific, daga kaso 10 zuwa 6 cikin dari a Latin Amurka da Caribbean, a yankin Saharar Afirka, duk da cewa ya ragu tsakanin shekarar 2008 zuwa 2012, ya karu da daga kaso 21.4 zuwa 23.9 cikin dari a shekarar 2012. Yankin Saharar Afirka ya fi ko wani yanki yawan yaran da ake bautarwa a doron kasa.