Kamfanonin jiragen sama sun dakatar da safara zuwa Isra'ila

Kamfanonin jiragen sama sun dakatar da safara zuwa Isra'ila

An sanar da cewa an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa zuwa Isra’ila saboda hare-haren roka daga Gaza zuwa wurare da dama a Isra’ila.

A cikin wani labarin a jaridar "Calcalist" da ke kasar Isra'ila ta wallafa, an bayyana cewa kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa sun dakatar da zirga-zirgar su zuwa Isra'ila kanfunan jiragen saman Isra'ila ne kawai yanzu ke zirga-zirgar cikin gida.

Rahoton ya lura cewa Filin jirgin sama na Ramon, wanda Isra’ila ke amfani da shi a madadin filin jirgin sama na Ben Gurion, a bude yake ga jiragen saman kasashen duniya, kuma kamfanoni ba sa son safara har sai Talata 18 ga Mayu.

A cikin bayanin da Hukumar Kula da Filin Jirgin Sama ta Isra’ila ta yi, an bayyana cewa, an soke tashin jirage 40 da aka shirya yi jiya daga filin tashi da saukar jiragen saman Isra’ila na Ben Gurion.

Kamfanin Royal Caribbean, kamfanin fasinjan jirgin ruwa na kasa da kasa, ya sanar da cewa ya dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwan zuwa Isra'ila daga Girka da Cyprus ta Girka.

A cikin bayanin da kamfanin ya yi, an sanar da cewa, an shirya fara zirga-zirgar ne daga tashar jirgin ruwan Isra’ila ta Haifa daga watan Yuni saboda dalilan tsaro


News Source:   ()