Kamfanin Pfizer ya fitar da sanarwa game da riga-kafin Corona

Kamfanin samar da magunguna na Pfizer da ke Amurka ya bayyana cewar sai nan da karshen watan Oktoba za su iya tabbatar da ko allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) da suke samarwa na aiki ko kuma akasin haka.

Shugaban kamfanin na Pfizer, Albert Bourla ya tattauna  da tashar talabijin ta CBS da ke Amurka, inda ya bayar da bayanai game da aiyukan samar da allurar riga-kafin Corona da kamfaninsu ke yi.

Ya ce "Idan aka gano allurar na da tasiri, to za a sake ta a kasuwanni nan da karshen shekara."

Bourla ya kuma ce sai nan da karshen watan Oktoba za su iya tabbatar da ko allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) da suke samarwa na aiki ko kuma akasin haka, kuma sun shirya rarraba allurar ga dukkan sassan duniya don sayarwa.

Ya ce, ya zuwa yanzu an shiga mataki na 3 na gwajin allurar a kan mutane dubu 30 masu shekaru daga 18 zuwa 85, kuma suna fatan kara yawan wadanda za a gwada allurar a kansu zuwa mutane dubu 44. Za kuma su gwada allurar riga-kafin a kan 'yan kasa da shekaru 16 da kuma wadanda suke dauke da munanan cututtuka.


News Source:   ()