Kamfanin jiragen sama na Buta Airways na kasar Azabaijan da ya dakatar da sufirinsa zuwa Istanbul saboda annobar Korona a ranar 14 ga watan Maris ya ci gaba da aiki.
A ranar 18 ga watan Maris ne dai zai dawo kan aiki inda zai rinka sufuri tsakanin filin Jirgin Saman Istanbul na Sabiha Gokce da na Baku a ranakun Litinin da Alhamis.
Kamfanin jirgin saman Buta gabanin annobar Korona yana sintiri sau 7 a sati tsakanin kasashen biyu.