Kamfanin Denmark zai samar da rigakafin Kyandar Biri miliyan 10

Kamfanin Denmark zai samar da rigakafin Kyandar Biri miliyan 10

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana kyawar cutar a matsayin annubar da ke buƙatar tunkarar gaggawa a duniya bayan ta yi mummunar yaɗuwa a nahiyar Afrika.

WHO ta kaɗu da yadda cutar ta Kyandar Birin ta yi ƙamari a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo har ma da wasu ƙasashe makwabtanta.

Yanzu haka dai kamfanin samar da magunguna na Bavarian Nordic na ƙasar Denmark ya ce,  yana da ƙarfin da zai iya samar da alluran rigakafin cutar har miliyan 2 a cikin wannan shekara ta 2024, sannan a jumulce, zai iya samar da miliyan 10 nan da shekara mai zuwa.

Kamfanin na jiran ƙarbar izini daga ƙasashen da wannan annuba ta dirar wa kafin fara aikin samar da rigakafin, yana mai cewa a  halin yanzu ma, yana da rigakafin da yawansa ya kai dubu 500 a ajiye.

Tuni dai hannun jarin wannan kamfanin ya samu ƙarin tagomashi da kashi 8 a wannan Alhamis a kasuwar hannayen jari ta Copenhagen sakamakon sanarwar da Huklumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi kan ɓarkewar annubar ta Kyandar Biri da kuma buƙatar ɗaukar matakan gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)