Mutane 60 sun raunana a lokacin da wata tankar dakon man fetur ta fashe a kan iyakar Afghanistan da Iran.
Wata mummunar fashewa ta faru lokacin da tankar mai dauke da mai ta isa mashigar da ke kan iyakar Iran.
Wutar da ta kama bayan fashewar tankar ta bazu a wani yanki mai fadi sosai cikin kankanin lokaci.
An tabbatar da cewa lamarın ya yı sanadıyar raunanan mutane 60 kuma motocin daukar marasa lafiya sun kasa tunkarar yankin na dogon lokaci saboda wutar.
Motoci sama da 500 sun kune kurmus inda suka zama toka, an yi hasarar miliyoyin daloli sakamakon afkuwar lamarin.