Kakakin Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya yi kira da a bayyana sunayen yara kanana Falasdinawa da Isra'ila ta kashe a Zirin Gaza a shafukan sada zumunta.
Kalin ya yada wani bidiyo cikin harshen Turanci da ke bayyana ya zuwa yanzu Isra'ila ta kashe yara kanana 61 a Zirin Gaza, kuma babu daya daga cikinsu da yake dan ta'adda.
A sakon, Kalin ya bayyana sunan yaro daya mai shekaru 4 da Isra'ila ta kashe.
Kalin ya kuma ce, wannan yaro da aka kashe ba zai dawo ba, kuma ya yi kira da a bayyana sunayen dukkan yaran da aka kashe.
Ya ce, "Ku fadi sunayensu tare da aikawa wasu."