Kakakin shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya gana da mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai Martin Griffiths.
A yayin taron da aka gudanar a Fadar Shugaban kasa, an tattauna yanayin jin kai da matsalolin agaji a Afghanistan da Siriya.
An jaddada mahimmancin karfafawa da tsarin sauyi na lumana don kada lamurra su kara tabarbarewar yanayin jin kai a Afghanistan. An bayyana gamsuwa da shawarar kwamitin sulhu, wanda ke tabbatar da ci gaba da ayyukan agaji a Siriya.
Ibrahim Kalin ya bayyana a taron cewa Turkiyya ba ta da damar da za ta iya kula da sabbin bakin haure tare da jaddada cewa ya kamata kasashen duniya su dauki mataki cikin gaggawa.
A yayin taron, an kuma bayyana cewa cimma matsayar siyasa yana da mahimmanci don kawo karshen rikicin jin kai a Siriya.
News Source: ()