Mai magana da ya yawun shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya mayar da martani ga kungiyar 'yan ta'addar aware ta YPG / PKK akan tsare matasa dubu 2 da 700 da tilasta musu daukar makamai a garin Hasakah dake Siriya.
A cikin bayanin nasa a shafinsa na Twitter, Kalin ya bayyana cewa a cikin watan Maris kungiyar ta'addancin aware ta YPG / PKK ta yi garkuwa da matasa 2,700 tare da tilasta musu daukar makamai a yankin garin Haseke dake kasar Siriya.
Kalin ya kara da cewa,
Ya kamata kasashen yamma su fahimci lamurkan YPG/PKK, ko wadanda ke basu gudunmowa zasu yi komai game da haka, babu abinda zasu iya cewa ga dukkan alamu.