Kalaman Erdogan akan zagayowar shekara ta 568 da kafa birnin Istanbul

Kalaman Erdogan akan zagayowar shekara ta 568 da kafa birnin Istanbul

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi murnar cika shekaru 568 da kafa Istanbul.

Shugaba Erdogan ya yada a shafinsa na Twitter da cewa,

"Ina taya murnar cikar shekaru 568 da Samun Nasara a Istanbul, daya daga cikin nasarorin da muka samu na tarihinmu. Ina tunawa da Fatih Sultan Mehmet Khan da rundunarsa mai daukaka, wadanda Annabinmu ya yaba musu kuma suka kafa wannan birni na musamman a tarihinmu cikin rahama da girmamawa."

A cikin sakon Erdogan, ya kara da cewa Annabi Muhammad (SAW) ya ce, "Babu shakka za kubutar da Istanbul. Wanda babban kwamanda mai tasiri zai jagoranta.
Shugaba Erdogan ya yada wannan sakon nasa tare da hoton Masallacin Hagia Sophia dake birnin Istanbul.


News Source:   ()