An sanar da samun matsalar bude shafukan kafar sadar da zumuntar Instagram a doron kasa.
Dangane ga kafar yanar gizon DownDetector, sama da masu amfani da Instagram 6,000 sun ba da rahoton samun matsalolin shigar manhajarsu.
Yayin da har yanzu ba a san musabbabin matsalar ba , kashi 51 cikin ɗari na waɗanda suka ba da rahoton matsalolin sun ce ba su iya samun damar shiga shafukansu ba, kashi 29 kuma sun bayyana rashin iya yada sakonni a shafukan , kashi 20 cikin ɗari sun ba da rahoton samun wasu matsaloli tare da gidan yanar gizon Instagram.
A shafin Twitter, wani dandalin sada zumunta, hashtag #instagramdown (Instagram ya rushe) ya zama daya daga cikin abin da ake magana akai.