Har zuwa yanzu dai Trudeau da kansa bai sanar da yiwuwar ajje aikin ba, sai dai wasu majiyoyi makusantan shi sun shidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters da Globe da kuma Mail cewa da safiyar yau Litinin Trudeau ke shirin miƙa takardun murabus don kawo ƙarshen zamansa a Ofis na shekaru 9.
Kai tsaye murabus ɗin na Trudeau zai kawo karshen jagorancinsa na jam’iyyar Liberal da ke ci gaba da mulkin ƙasar ta nahiyar Amurka.
Murabus ɗin Trudeau kai tsaye zai jefa jam’iyyar ta Liberal a tarin matsaloli musamman na rashin jagora a wani yanayi da ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ke nuna cewa tabbas jam’iyyar za ta sha kaye a hannun abokiyar adawarta ta Conservatives wato masu ra’ayin ƴan mazan jiya matuƙar aka kira zaɓe.
Bisa ƙa’ida a ƙarshen watan Oktoban shekarar nan ne Canada za ta gudanar da babban zaɓenta, kuma babu tabbacin Liberal mai tsaka-tsakan ra’ayi ta iya farfaɗowa daga koma bayan da ta samu gabanin wannan lokaci.
Majiyoyin sun ce ko da Trudeau bai sanar da murabus a yau Litinin ba, ko shakka babu zai aiwatar da hakan gabanin taron ƴan majalisun jam’iyyar ta shi ta Liberal a ranar Larabar makon nan.
Jam’iyyar ta Liberal da kanta ta matsa lamba ga Trudeau wajen ganin ya yi murabus daga shugabancinta, sai dai babu tabbacin ko shugaban zai ajje dukkanin aikin lokacci guda ko kuwa zai ci gaba da jagorantar Canada har zuwa lokacin da Liberal za ta zaɓi sabon shugaba.
Trudeau wanda ya fara jagorancin Canada a shekarar 2013 matuƙar murabus ɗin na sa ya tabbata kenan Liberal na buƙatar zaɓen jajirtaccen jagoran da zai buga da Donald Trump na Amurka ganin yadda ƙasashen biyu maƙwabtan juna suka shiga gagarumin rikicin a wa’adin Trump na farko.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI