Joe Biden ya yiwa matalautan ƙasashe alkawarin tallafin dala biliyan 4

Joe Biden ya yiwa matalautan ƙasashe alkawarin tallafin dala biliyan 4

Ɗaya daga cikin manyan jami’an Amurka ne ya bayyana wannan albishir ga manema labarai a birnin Rio, inda ya ce  Biden ya sha alwashin bayar da tallafin biliyoyin dalar ne jiya Litinin, bayan fara taron ƙasashen G20 wanda ake ƙarƙare shi a yau.

A cewar jami’in, yanzu haka an fara tattaunawa tsakanin masu kula da baitulmalin Amurka da kuma Bankin Duniyar kan shirin ƙarfafa asusun nasa na taimakawa ƙasashe matalauta, wanda shugaba Biden ɗin ya bai wa tallafin dala biliyan $3.5 a watan Disambar shekarar 2021.

Sai dai babu tabbbas kan ko shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump zai cika alƙawarin da shugaba Biden mai barin gado ya ɗauka ba, la’akari da cewa rage yawan kuɗaɗen tallafin da Amurka ke baiwa ƙasashe na daga cikin manyan manufofin da Trump ɗin yayi alƙawarin aiwatarwa da zarar ya kama aiki.

Wannna ta sanya manema labarai tuntuɓar kakakin kwamitin shugaba Donald Trump dake kula da shirin karɓar mulki daga gwamnatin Biden, sai dai yayi gum da bakinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)