Jirgin yakin Rasha mai saukar ungulu kirar Mi8 ya keta hakkin sararin samaniyar Japan inda ya shiga ba bisa izini ba yankin Hokkaido.
Ma'aikatar tsaron kasar Japan, ce ta sanar da cewa jorgin yakin Rasha mai saukar ungulu kirar Mi8 ya keta hakkin sararin samniyarta a yankin gabashin Shiretoko.
An sanar da cewa jirgin ya shiga yankin ne bisa kuskure inda ya fice daga yankijn nan take bayan jan kunne daga ma'aikatar tsaron Japan.
Ma'aikatar tsaron kasar Japan ta nuna rashin jin dadinta ga Moscow game da afkuwar lamarin.