Wani jirgin sama na yaki samfurin F-15C mallakar Amurka ya fado a Ingila a lokacinda yake tsaka da bayar da horo.
Sanarwar da aka fitar daga sansanin sojin saman Amurka na Lakebheath ta ce jirgin samfurin F-15C ya fado a tekun arewa da misalin karfe 09:40.
Sanarwar ta ce jirgin ya tashi daga sansani Lakenheath kuma ya yi hatsari a lokacinda yake tsaka da bayar da horon da ya saba.
Sanarwar ba ta bayar da bayanai game da matukin kirgin da musabbabin hatsarin ba, kuma an bukaci taimako daga jami'an ceto na Ingila.