Wani jirgin saman soja dauke da mutane 85 ya yi hadari a lardin Sulu da ke kudancin Philippines. Akalla mutane 40 aka ceto daga tarkacen jirgin da ya faɗi.
Janar Cirilito Sobejana, Babban hafsan hafsoshin Philippines, ya sanar da cewa jirgin sojan ya fadi ne yayin da yake kokarin sauka a tsibirin Jolo da ke lardin Sulu.
Da yake bayyana cewa an ceto mutane 40 ya zuwa yanzu, Janar Sobejana ya ce,
"Kungiyoyin bincike da ceto na ci gaba da aiki a yankin domin ceton rayukan sauran wadanda suka tsira,"
An samu labarin cewa jirgin na tafiya ne domin daukar sabbin daliban da suka kammala karatunsu na makarantar sojan zuwa wurin aiki.