Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Alaska ta Amurka.
Ba a san musabbabin fadowar jirgin saman samfurin Eurocopter AS50 a yankin Knik mai dusar kankara ba.
Mutane 5 sun mutu sakamakon fadowar jirgin. Wani mutum 1 ya samu munanan raunuka.
An aika da jami'an ceto daga Cibiyar Ceto ta Alaska zuwa wajen da hatsarin ya afku.
Ba a riga an bayyana sunayen wadanda suka mutu ba, kuma Hukumar Tsaron Sufuri ta Kasa ta fara gudanar da bincike.