Karamin jirgi mai saukar ungula, Ingenuity wanda Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta aika zuwa duniyar Mars ya samu nasarar kammala aikinsa na 4 a yau.
Jami'an NASA sun sanar da cewa jirgin mai saukar ungulu ya yi tafiyar mita 266 a gudun kilomita 13 cikin sa'a guda a tafiyarsa na karshe.
Jami'an sun bayyana cewa balaguron ya dauki tsawon dakika 117 kuma ya nuna karfin jirgin na iya yin aiki a matsayin jami'in leken asiri a duniyar Mars.
Kumbon Perseverance da ya sauka a Jezero Crater a ranar 18 ga Fabrairu ne ya kai Ingenuity zuwa duniyar Mars.