An sanar da cewa jirgin fasinja mallakar kanfanin Sriwijaya ya fada jikin teku dauke da ma'aikata 12 da fasinjoji 50.
Kamar yadda ministan sufurin kasar Budi Karya Sumadi ya sanarwa manema labarai da cewa signal din jirgin mai lamba "SJ182" ya katse bayan mintuna biyar da tashinsa.
Ya kara da cewa jirgin ya fado ne a yankin tsibirin Laki da Lancand dake arewacin babban birnin kasar Jakata.
Sumadi ya bayyana cewa tuni dai ma'aikatan ceto sun bayyana a yankin domin fara aikin ceto.