Wani jirgin ruwan dakon kaya na Iran ya kife a gabar tekun Iraki. An kubutar da ma'akatansa 4 inda ake cigaba da neman sauran.
Labaran da kafafan yada labaraina yankin suka fitar sun ce jirgin ruwan Iran mai suna "Behbehan" ya kife a mashigar teku ta Basra da ke kusa da hanyar Hor Abdullah.
Jirgin ya kife da tsakar dare kuma ba a san musabbabin hatsarin ba.
Mataimakin gwamnan Basra kuma tsohon Ministan Sufuri na Iraki Kazim Fincan ya shaida cewar an kubutar da ma'aikatan jirgin 4 kuma ana ci gaba da aiyukan kubutar da wasu 5.