Mutane 14 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijira a gabar tekun Venezuela.
Yara kanana 2 na daga cikin 'yan gudun hijirar da suka mutu a bayan kifewar jirgin ruwan da ke kan hanyar zuwa Trinidad da Tobago.
Rukunin wadanda ke cikin jirgin sun tashi daga garin Guiria na jihar Sucre da ke arewa maso-gabashin Venezuela a ranar 6 ga Disamba.
Hukumar Magance Gudun Hijira ta Kasa da Kasa (IOM) ta bayyana cewar, a kalla mutane miliyan 5,4 suka gudu daga Venzuela saboda rikicin siyasa da matsin tattalin arziki.
'Yan gudun hijirar Venezuela na guduwa zuwa kasashen Latin Amurka da Carribean.
A shekarar da ta gabata a kalla jiragen ruwa 2 ne suka bata a teku a lokacin da suke tafiya zuwa Trinidad da Tobago.