Mutane 14 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar jirgin ruwa a gabar tekun kasar Haiti.
Sanarwar da jami'in ofishin kare fararen hula na arewa maso-yammacin Haiti Jose Rethone ya fitar ta ce jirgin ruwa dauke da mutanen da suka halarci kasuwar yankin Saint-Louis-du-Nord ne ya kife a kan hanyarsa ta dawowa Tsaunin Tortuga ya kife.
Rethone ya ce an kubutar da mutane 9 inda wasu 14 kuma suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin. Wasu da dama kuma sun bata.
Rethone ya kara dacewar jami'an tsaron teku na Haiti ba su kai dauki ga bukatar neman taimakon da mutanen suka nema ba, inda suka nemai taimakon na Amurka.