Mutane 16 sun rasa rayukansu sakamakon tatsile 'yan gudun hijira da wani jirgin kasa na dakon kaya ya yi a jihar Maharashtra da ke Indiya.
Labaran da jaridun Indiya suka fitar sun ce, wasu'yan gudun hijira su 20 ne kwanta a kan karafan layin dogo don hutawa a garin Evrengabad a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gidajensu a kafa sakamakon dokar hana fita da aka saka a Indiya.
Mahukunta sun ce duk da jirgin dakon kayan ya ga 'yan gudun hijirar leburori a kwance amma sai da ya bi ta kansu wanda hakan ya yi ajalin 16 daga cikinsu
'Yan sanda na tunanin cewar 'yan gudun hijirar sun kwanta a kan layin dogon ne saboda tunanin ba za a samu safarar jirgin kasa sakamakon saka dokar hana fita.
An fara gudanar da bincike kan lamarin.
Tun ranar 25 ga Maris aka saka dokar hana fita a Indiya wanda ahakan ya bar 'yan gudun hijira lebrori a kan tituna.
Jiragen kasa da motocin da gwamnati ta samar na kwashe 'yan gudun hijira leburori zuwa garuruwansu ba su isa ba.