Jirgi mara matuki kirar Bayraktar TB2 na kasar Turkiyya ya kafa tarihi

a Hukumar T3 Selcuk Bayraktar ya bayyana cewar jirgi mara matuki kirar Bayraktar TB2 ya kafa tarihi inda ya yi shawagin awanni dubu 200 a sararin samaniyya.

Selçuk Bayraktar, ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa jirgin ya kafa tarihin a harkokin sararin samaniyyar kasar Turkiyya wanda ba'a taba samun jirgin kasar da ya yi haka ba.

Bayraktar, ya kara da cewa,

""Bayraktar TB2, ya yi sa'o'i dubu 200 ya na shawagi cikin haƙuri, ƙauna da juriya a sararin samaniyar Turkiyya. Wannan shi ne mafi tsawo sa'o'i da wani jirgin kasar Tuirkiyya ya bata yi yana shawagi a sararin samaniyya"

 


News Source:   www.trt.net.tr